Lamborghini Huracán LP 610-4 t
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da
Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha biyar


Sayyed Zakzaky2

Yaya matsayin riba yake a al'amarin kasuwanci?
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Yaya hukuncin azumi ga direban da yake tafiya kamar daga Abuja zuwa Kano kullum?

Daga Bashir Salisu Tudun Jukun Zariya

SHAIKH ZAKZAKY: Idan mutum sana'arsa ce tafiya din, to shi ba ya kasarun salla, kuma yana yin azumi. Kamar direba kenan wanda shi sana'arsa ce, kuma kulluyaumin yana kan tafiya din. In yana daukar fasinjoji kenan. Shi mota din tamkar gida take a gurinsa. Amma idan matafiyi ne kawai, wanda kulluyaumin tafiyar tana kai shi Abuja din ne zuwa Kano, ba a matsayin sana'arsa ce tafiyar ba kamar direba, wato shi yakan je ne kamar ya yi kasuwanci ko ya yi aiki ya dawo, to shi wannan zai sha azumi kuma zai yi kasaru.


TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Wadanne addu'o'i zan yi da za su taimaka min wajen ayyukan da za su shagaltar da ni ga aikata alheri da umurni da alheri, ta yadda Shaidan da danginsa ba za su taba samun galaba a kaina ba?

Daga Sakinat Ibrahim Gwadabe Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Ma'asurat sun wadace ki. Ma'asurat na addu'o'in kowace rana da kowane dare. Kamar akwai addu'o'in da ke cikin Diya'u Salihin, wanda ya kawo ayyukan rana-rana daga Asabar zuwa Juma'a da kuma addu'o'in kowace rana na wata, daga 1 ga wata har zuwa 30 ga wata. Shigen irin wannan kuma akwai Misbahul Mutahajjud, sai dai ba na wata. A ciki an nemi kariya daga dukkan sharri, an kuma roki dukkan alheri.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Menene hukuncin mutumin da ya yi karya alhalin yana azumi?

Daga Dahiru Ibrahim Gyallesu Zariya

SHAIKH ZAKZAKY: Karya dai haramun ne, mutum yana azumi ko ba ya azumi. Sai dai in mutum yana azumi ana cewa mutum ya yi azumin ido da na baki da sauran gabubba. Saboda haka ka ga kenan karyar a nan ta fi girman laifi. Kuma akwai wani nau'in karya wanda shi yana karya azumi. Shi ne in ya yi wa Allah karya, ko ya yi wa Manzon Allah karya. Amma sauran karya in ba wacce aka yi wa Allah da Manzonsa da Ma'asumai ba, to zai zama ya aikata haramun ne.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Yaya matsayin wanda ya yi sahur ko buda baki da abincin haram?

Daga Dahiru Ibrahim Gyallesu Zariya

SHAIKH ZAKZAKY: Shi ma kamar wancan, haramcin ya dada karuwa kenan. Amma dai haramun ne. Idan ya yi sahur da haram ya aikata haram, idan ya yi buda baki da haram, ya aikata haram. Amma za mu iya cewa azuminsa na nan. Sai dai ya inganta a shari'ance ba yana nufin ya karbu a wajen Allah bane. Karbuwa a wajen Allah wani abu ne gaibu, amma hukunci zahiri na shari'a azuminsa yana nan, amma tana iya yiwuwa ba a karba ba ma. Amma idan mutum ya karya azumi da haram, kamar misali ya sha giya ko ya ci naman alade da rana a watan Ramadan, to shi ana lizimta masa kaffara biyu. Da kaffarar karya azumi da kuma kaffarar karya shi da haramun.

TAMBAYA: Akramakallahu. Menene hukuncin rubuta sunan Allah a takarda ko wani abu alhali an san wannan abin zai iya kai wa ga hannun wanda ba musulmi ba? Daga Baban Bara'atu Al-Dambamy

SHAIKH ZAKZAKY: Ba a girmama sunan Allah din ba kenan. Ana son ya kasance a kiyaye sunan Allah da sunan Annabawa da sunan A'imma, ta yadda mutum musulmi ma ba a yarda ya taba wadannan ba sai idan yana da alwala, to ballantana kuma yana da masaniyar cewa za shi ga hannun wanda yake shi ba musulmi bane. Saboda haka sai mu ce yin haka nan ya haramta.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Menene hukuncin mutumin da yake yin yanka na dabbobi ana biyan sa?

Daga M. Bayero Fuddiya Giade Bauci

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle wannan ba wani laifi a ciki. Tunda yake ba 'fard ain' bane. Faralin aini ne mutum ba a biyan sa lada in ya yi. Ko ma faralin kifaya, ba a biyan mutum lada in ya yi. Kamar misali wanke mamaci, wanda yake ya hau kan al'ummar musulmi, amma in wasu suka yi, sun dauke wa sauran. Shi kuwa yanka dabba ba farali ne da ya hau kan kowa ba, yana dai cikin ladubban yanka cewa yana cikin abin da yake halas da haram. Haramun ne a ci dabbar da ba a yanka ba. Saboda haka abin da yake aikatawa halas ne. In ya zama an dauke shi aiki, lasiman ma aka ce shi aikin da zai rika yi kenan, an hana shi ya yi wani aiki, zai zama lazim a biya shi lada. Ta wannan fuska kana iya cewa Liman, in aka yanka masa albashi ba ana biyan sa ladan sallar da ya yi bane, ana biyan sa ladan an hana shi ya shagalta da wasu ayyuka ne don ya shagalta da wannan. Saboda haka ka ga ba ladan salla kenan ya karba ba.

TAMBAYA: Shin wajibi ne idan za a yi yanka a juyar da fuskar dabbar gabas ko kuwa, kuma mene ne hujjar yin hakan?

Daga M. Bayero Fudiyya Giade Bauci SHAIKH ZAKZAKY: Yana cikin adab ne, ladubban yanka, fuskantar da ita dabbar alkibla in zai yi yanka. Amma idan saboda wani dalili ya faskara, to ko da da gangan ana iya juyawa zuwa wani wuri. In kuma bisa kuskure aka yi yankan ba a kalli alkiblar ba, duk dai yanka ya yi.

TAMBAYA: Masu mata biyu sukan yi wani abu, idan matar su daya ta haihu sai su koma dakin daya har sai wannan ta yi arba'in, to mene ne hukuncin wannan?

Daga Haruna mai shinkafa Giade Bauci

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle a shari'a ba a ce haka nan ba. Rabon kwana yana nan kamar yadda yake kafin ta haihu da bayan ta haihu. Ba a ce in tana misali haila ko nifasi, sai a ba wata kwananta ba. Ballantana a ce kuma in wannan ta haihu, kwana 40, kwanan ya koma wajen wata. Rabon kwanan na nan. Sai dai idan ita wadda ta haihun ne ta ce ta ba kishiyarta nata kwanakin. A hukunci ba a ce hakkin shi maigida ne ya koma ga wata, ya kyale wannan a yayin da take haila, ko nifasi, ko take reno ba.

TAMBAYA: Ni ina sayar da Almizan ne kuma wadanda ba musulmi ba suna saya a wajena, shin ya halasta in rika sayar masu duk da cewa akwai sunan Allah ko kuwa?

Daga Haruna mai Shinkafa Giade bauci

SHAIKH ZAKZAKY: Ba laifi sai da musu, saboda ko ba komai rubutu ne wanda aka yi da haruffan boko. Kuma ko da da sunan Allah da ma ayoyin Alkur'ani, fassararsu, duk babu laifi, domin akwai in aka rubuta takarda ma zuwa ga kafiri, ana iya kawo aya. Bai zama takardar ta koma ayar Alkur'ani ba, don mus'hafin Alkur'ani aka hana. Muna da kyakkyawan misali ma daga wasikar da Manzon Allah ya rubuta wa Sarkin Sham. A ciki ya kawo ayar Alkur'ani - "Kul ya Ahlul kitabi ta'alau ilaЕ." Cikakkiyar ayar. Ga shi kuma an rubuta zuwa ga kafiri. Har ma kwafin wannan wasika ta Manzon Allah yanzu ana ganin ta. Wannan ya nuna rubuta wa kafiri takarda, a kawo masa hujja da aya babu laifi a ciki. Saboda haka kasantuwar Almizan akwai ayoyi da hadisai, duk ba zai hana a ba kafiri ba. Wato mus'hafin Alkur'ani da hadisi sosai shi ne ba za a iya ba shi ba.

TAMBAYA: Tambayata a nan ita ce Malam ya ce idan adilai biyu sun ga wata, to ana iya daukar azumi,to shin idan Sarkin musulmi ya ce an gani, to ana iya dauka?

Daga Aminu Adamu Tudun Wada Zariya

SHAIKH ZAKZAKY: Ko wanene ma Sarkin musulmi din, idan yana ba ka labarin ganin adilai ne, to shi kenan ya zama mai ba da labari, kamar yadda rediyo na iya ba ka labari ko jarida ko takarda ko tarho. Ka ga ana ba ka labarin tabbacin ganin adilai ne, ba shi wanda ya kira Sarkin musulmin kawai ya ce kawai an gani ne ba. Yana batun ganin adilai ne. A kan wannan sai a ce tamkar shi mai ba da labari ne. Kuma an yarda cewa ana iya ba da labarin ganin wata ta hanyar aloli na zamani kamar tarho ko rediyo, kuma ya inganta. Ba lale sai adilan da suka gani lazim sune za su gaya maka ba.

TAMBAYA: Allah shi gafarta Malam, yaya matsayin riiba yake a al'amarin kasuwanci, da gaske ne idan mutum ya dora ko nawa ne, riiba ne ba riba ba?

Daga Abubakar Giginyu Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Riba tana samuwa ne a kan an dora wani kari a kan a kan abin da ya hau kan mutum ya biya bashi. Shi kuwa riiba bambanci ne tsakanin yadda mutum ya siyo kaya da kuma dawainiyar da ya zuba a kan kayan da kuma yadda ya sayar. Don haka in an fid da uwar kudi, abin da ya hau shi ake ce wa riiba. Lalle shari'a ba ta kayyade cewa ga iyakar abin da ake dorawa ba, kamar a ce in an kwatanta da uwar kudin, ba a ce ka dora kaza bisa dari ba misali. Amma akwai riibar da in ta yi tsanani ta zama haramun, kazamar riiba kenan. Ko ta zama kazamar riiba, ta zama haramun ba sunan ta riba ba, kodayake ta haramta. Idan riiba ta zama da cuta, misali ka sai abu kuma ya kamata a ce abin da ka daura kamar nunkinta daya ne ganin wahalar da ka yi daga inda ka sayo zuwa inda ka sayar, amma sai ka nunka shi sau biyar misali, alhali da mutumin da zai saya ya san yadda ka sayo da dawainiyar da ka yi, da bai yarda ya saya a yadda ka sayar masa ba. Zai zama ka kware shi, saboda haka ka ci kazamiyar riiba, wacce ta haramta. Amma ba sunanta riba bane. Ko da muka ce ba riba ce ba, ba muna nufin ta kowane hali duk riibar da mutum ya dora a kan kayansa ya halasta bane. Yana iya yin tsananin da zai zama haram.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din